Jam’iyun PDM da ADC a Niger sun haɗe da NNPP

Jam’iyun PDM da ADC sun hade da jam’iyar NNPP a jihar Niger.

Hakan na zuwa ne biyo bayan hukuncin da kotun koli ta yanke da ya tabbatar da ikon da hukumar zabe ta INEC take da shi na soke jam’iyun da suka gaza tabuka abun azo a gani a zabubbuka.

Jam’iyun siyasa 22 hukumar ta INEC ta soke inda suka garzaya kotu suna kalubalantar matakin na INEC har ta kai ga kotun koli.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa jam’iyun biyu ta bakin shugabanninsu, Engr Abdullahi Abubakar Gwada na PDM da Yahaya Adamu na ADC sun bayyana cewa suna sane da tasirin da hukuncin kotun kolin yake da shi.

Tuni suka umarci magoya bayansu da su fara rijista a jam’iyyar NNPP.

More News

DA ƊUMI-ƊUMI: DSS sun cafke Sowore a filin jirgin na Legas

Jami'an Hukumar Ƴansandan Farin-kaya ta DSS sun kama Omoyele Sowore, jagoran kungiyar  #RevolutionNow Movement da ke adawa da gwamnati a filin jirgin sama na...

Ƴan bindiga sun ƙone ginin hedkwatar ƙaramar hukuma tare da kashe jami’an tsaro

Ƴan bindiga sun kai farmaki hedkwatar ƙaramar hukumar, Isiala Mbano dake jihar Imo da tsakar daren ranar 3 ga watan Satumba inda suka ƙone...

An kama wasu ƴanta’adda da ke da alaƙa da Turji

Akalla mayaka 18 da ke da alaka da fitaccen shugaban ‘yan ta’adda Bello Turji aka kama a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin...

Dakarun Najeriya sun kai farmaki wa ƴan’adda a Borno, wani kwamanda ya miƙa wuya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar a ranar Lahadin cewa dakarunta sun yi nasarar kashe wani fitaccen kwamandan kungiyar Boko Haram, Abu Rijab da wasu...