Jam’iyar ta sake tsunduma cikin rikici bayan wani hukuncin kotu

Babbar kotun tarayya dake Ibadan babban birnin jihar Oyo ta soke babban taron jam’iyyar PDP da aka yi ranar 15 ga watan Nuwamba a jihar inda aka zaɓi sababbin shugabannin jam’iyar.

A hukuncin da kotun ta yanke ranar Juma’a, Uche Agomoh alkalin kotun ya hana shugabannin jam’iyar da aka zaba wurin taron ayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyar

Agomoh ya bayyana cewa babban taron zaben shugabannin jam’iyar da aka gudanar a cikin watan Nuwamba ya saba umarnin da kotun ta bayar na kada a gudanar da shi.

Alkalin ya zartar cewa za a iya jagorantar jam’iyar PDP ne kaɗai ta hanyar shugabancin kwamitin riko har ya zuwa lokacin da za a gudanar da wani babban taron na zaɓen shugabanni.

Tsagin jam’iyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki wanda  aka zaba a  wurin taron su ne su ka shigar da kara gaban kotun inda suka nemi ta ayyana su a matsayin a matsayin halastattun shugab

More from this stream

Recomended