Jam’iyar PDP ta kori Nyesom, Fayose, Anyanwu da wasu mutane

Jam’iyar PDP ta kori tsohon gwamnan jihar Rivers kuma ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike tare da wasu mutane daga jam’iyar.

Jam’iyar ta dauki matakin korar ta su ne a wurin babban taron zaben shugabannin jam’iyar da ake gudanarwa a Ibadan babban birnin jihar Oyo.

Sauran mutane da jam’iyar ta kora sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose, tsohon sakataren jam’iyar, Samuel Anyanwu. Umar Bature, Adeyemi Ajibade, Mohammed Abdulrahaman, Sanata Mao Ohuabunwa, Austin Nwachukwu, Abraham Amer, George Turner  da kuma Cif Dan Orbih.

Tsohon mataimakin shugaban jam’iyar shiyar kudu, Olabode George shi ne ya gabatar da kudirin korar mutanen inda  ya samu goyon, Hon Sama’ila Burga shugaban jam’iyar PDP na jihar Bauchi.

Tunda farko tsagin jam’iyar dake biyayya da Wike sun nemi dakatar da babban taron ta hanyar shiga da karar gaban kotu sai dai jam’iyar PDP ta samu sahalewar yin taron daga wata kotu dake birnin Ibadan.

More from this stream

Recomended