Jam’iyar APC ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin jihar Kebbi

Jam’iyar APC ta lashe dukkanin kujerun shugabannin ƙananan hukumomi dana kansiloli a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a jihar Kebbi a ranar Asabar.

Aliyu Muhammad Mera Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kebbi(KESIEC) shi ne ya tabbatar da sakamakon zaɓen a wurin wani taron manema labarai ranar Lahadi a birnin Kebbi.

“APC ta lashe dukkanin kujerun ciyamomi da na kansiloli kamar yadda sakamakon zaɓen da aka tattara daga ƙananan hukumomi 21 da aka yi zaɓen ya nuna,” Mera ya bayyana.

Jam’iyar adawa ta PDP bata shiga zaɓen ba  bayan da tayi zargin cewa shugabannin hukumar ta KESIEC na da alaƙa da jam’iyar APC.

A yayin miƙa takardar shedar cin zaɓe ga zaɓaɓɓun shugabannin Mera ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓe cikin tsari inda ya jaddada cewa ya yi dai-dai da yadda doka ta tsara.

More from this stream

Recomended