Jam’iyar APC a jihar Kebbi ta kaddamar da yaƙin zaɓen Tinubu da gwamna Idris a 2027

Jam’iyar APC a jihar Kebbi ta kaddamar da yaƙin  sake zaɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu da kuma gwamnan jihar Nasiru Idris gabanin zaɓen shekarar 2027.

A wani babban taron gangamin siyasa da aka yiwa laƙabi da ” Muna bayan Tinubu da Kauran Gwandu” da ya gudana a babban birnin filin wasa na birnin Kebbi da ya samu halartar fitattun mutane ciki har da ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Abubakar Bagudu, gwamna Nasiru Idris, James Faleke da kuma ƙaramin ministan ma’aikatar ilimi,  Yusuf Tanko Sununu.

Da yake jawabi a wurin taron, Bagudu  yace da Tinubu da  Nasir Idris sun cancanta a sake zabensu a zango na biyu duba da irin ƙokarin da suka yi a cikin ƙasa da shekaru biyu da suka yi akan mulki.

Bagudu ya sanar da da bada gudunmawar miliyan ₦450 domin sayen kayan abinci a mazabun  jihar 225 domin rabawa a lokacin a azumi.

A nasa jawabin gwamna Nasiru Idris ya jaddada goyon bayan da jihar take bawa shugaban ƙasa Tinubu inda ya yabawa gwamnatinsa kan gudunmawar da take bayarwa wajen cigaban jihar Kebbi.

More from this stream

Recomended