Jami`o`in Najeriya na kokawa kan yadda dokokin ƙasar suka yi musu dabaibayi

BUK

Yayin da ɓangaren ilimi a Najeriya ke fuskantar tarin matsaloli da a lokuta da dama ke janyo dakatar da karatun ɗalibai saboda yajin aiki, jami’o’i a ƙasar na kokawa kan yadda dokokin ƙasar ke takure su, duk da yake a hukumance an ba su damar cin gashin-kansu.

Irin wannan takurawar ta haɗa da doguwar hanyar da jami`o`in ke bi don ɗaukar ma`aikata da biyan haƙƙoƙinsu.

Lamarin dai ya sa shugabannin hukumomin gudanarwar jami`o`in Najeriya sun fara wani yunƙuri na bitar dokokin don yi musu gyaran-fuska, ta yadda za su bada damar tafiya da harkokin yadda ake ganin ya dace.

Shugaban hukumar gudanarwar jami`ar Tarayya Ta Kashere, kuma ɗaya daga cikin ƴan kwamitin gyaran-fuska ga dokar, Yakubu Ruba, ya shaida wa BBC cewa dokokin da ake da su a yanzu suna hana ruwa gudu.

A cewarsa a halin da ake ciki adadin daliban da ake da su a jami’o’i kullum karuwa suke, don haka akwai bukatar daukar karin ma’aikata da malamai, ta yadda za a iya gudanar da aikin.

”Jami’ar da take ɗaukar ɗalibai dubu uku, ko dubu biyar, amma yanzu za ka ga wata tana da ɗalibai dubu goma ko dubu 20, amma a yanzu haka jami’o’i ba za su iya daukar ma’aikata a kashin kansu ba, sai sun je hukumar kula da jami’o’i ta kasa, daga nan kuma sai an je ofishin shugaban ma’aikata na Najeriya, to wadannan abubuwa ne da ya kamata a ce an yi gyara a kai”

Ya kara da cewa ”Dokar ta dukunkune jami’oin, kuma bata yi wani ƙarin bayani ba, ya kamata a ce ta kalli bukatun da ake da su sannan ta warware irin wadannan matsaloli da ake da su”.

A cewar Yakubu Ruba ”Idan ka ce jami’a tana da ikon cin gashin kanta, amma ba za ta iya yin komi a kashin kanta ba to ai an yi ba a yi ba, ya kamata a ce idan kana da yanci ya kasance za ka iya yin komi da kanka”.

More from this stream

Recomended