Jami’ar sufuri ta Daura ta shirya tsaf don fara karatu

Jami’ar Sufuri ta Muhammadu Buhari da ke Daura a Jihar Katsina na gab da kaddamar da ayyukanta don fara karatu har zuwa lokacin da Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa (NUC) ta gama amincewa da ita.

A yayin wata ziyara, tawagar NUC ta tabbatar da samar da kayan aikin da suka kai a fara karatun na.zangon 2023/2024.

Farfesa Umar Adam-Katsayal, mataimakin shugaban jami’ar na farko, ya nuna farin cikinsa, inda ya ce, “A shirye muke mu fara karatu.da zarar NUC ta amince da hakan.

Jami’ar ta ba da shawarar shirye-shiryen ilimi iri-iri don farawa.

Cibiyar tana jiran amincewar NUC don fara karatu nan take.

More from this stream

Recomended