Jami’ar Bayero ta fito da tsarin sama wa ɗalibai aiki a cikin makaranta

Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Sagir Adamu- Abbas, ya bayyana cewa cibiyar ta bullo da tsarin samar da aikin yi ga dalibai.

Adamu-Abbas ya ce jami’ar ta dauki nauyin dalibai don gudanar da wasu ayyuka a cibiyar, kuma suna biyan N15,000 duk wata.

Ya yi wannan jawabi ne a karshen makon da ya gabata a Kano lokacin da ya karbi bakuncin tawagar kungiyar masu aiko da rahotanni ta kasa (ECAN) a babbar harabar jami’ar.

Adamu-Sagir ya ce: “Jami’ar ma ta bullo da wani nau’in tsarin yi wa dalibai aikin yi, inda suka dau nauyin gudanar da wasu ayyuka a jami’ar kuma ana biyan su Naira 15,000 duk wata.”

Da yake magana kan karin kudin rijistar, shugaban jami’ar ya koka kan yadda ake kashe kudaden gudanarwa, musamman tsadar samar da wutar lantarki.

Ya bayyana cewa kudin wutar lantarkin ya kai kusan Naira miliyan 35 duk wata, yayin da kudin sayen dizal na janareta ya kai kimanin Naira miliyan 40.

Adamu-Abbas ya ce dole ne hukumar ta kara yawan rijistar, saboda a zahiri abu ne mai wuya a samar da ayyukan jin dadin jama’a ga dalibai kusan 45,000 da suka hada da wadanda suka kammala digiri, da ma’aikata sama da 5,000, na koyarwa da wadanda ba sa koyarwa.

More from this stream

Recomended