
Jami’an rundunar yan sandan Najeriya sun rufe ginin hedkwatar jam’iyar PDP dake Abuja.
Rufe ginin hedkwatar jam’iyar ta PDP na zuwa ne biyo bayan tashin hankalin da aka samu a ranar Talata inda tsagin jam’iyar biyu suka barke da rikici lokacin da suke ƙoƙarin kwace iko da ginin hedkwatar jam’iyar.
Wani fefan bidiyo da aka yada a ranar Laraba ya nuna yadda aka zagaye ginin hedkwatar jam’iyar da waya mai yanka hannu domin hana shiga ko fita daga cikin ginin.
An jibge tarin jami’an tsaro a wurin domin tabbatar da babu wanda ya karya dokar hana shiga ginin.
Babu ko mutum guda daga cikin shugabannin tsagin biyu da aka gani a ginin sakatariyar jam’iyar tun bayan rikicin na ranar Talata.
Kawo yanzu dai tsagi biyu da suka hada da na ministan Abuja, Nyesom Wike da kuma na sabon shugaban jam’iyyar Kabiru Tanimu Turaki ke ikirari da iko da jam’iyar ta PDP.

