
Gawurtaccen dan bindiga da ake kira da Yellow Danbokkolo ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a wata fafatawa da suka yi da jami’an tsaro.
Danbokkolo ya shafe tsawon lokaci yana addabar al’ummomin yankin gabashin jihar Sokoto.
A cewar mai bawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu shawara kan gidajen jaridu, Abdulaziz Abdulaziz marigayin ya mutu ne a ranar Lahadi a sakamakon raunukan da ya samu a wata fafatawa da jami’an tsaro a makon da ya gabata
Abdulaziz ya ce mutane da dama na ganin cewa an fi tsoron Danbokkolo akan gawurtaccen dan bindiga, Bello Turji saboda rashin tausayinsa
Daya daga cikin ta’asa mai muni da Danbokkolo ya aikata ita ce ta kona wasu fasinjoji a yankin Shinkafi na jihar Zamfara.