Jami’an tsaro sun kashe ƴan ƙungiyar IPOB 5 a Anambra

Jami’an tsaro a jihar Anambra sun kashe wasu mutane biyar da ake zargin mambobin kungiyar IPOB ne dake fafutukar kafa ƙasar Biafra a garin Ufuma dake ƙaramar hukumar Orumba North a jihar Anambra.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar,Ikenga Tochukwu ya bayyana cewa wata tawagar jami’an tsaro da ta ƙunshi sojoji, ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro sun samu nasarar kai wani samame a ranar 14 ga watan Janairu da misalin ƙarfe 12:30 na rana a maɓoyar yan bindigar dake kan titin Umugem dake Ufuma a ƙaramar hukumar Orumba North.

Ya ce tawagar sun samu nasarar harbe ƴan bindiga biyar nan take a yayin da wasunsu suka tsere da raunin harbin bindiga.

Ya ƙara da cewa a yayin farmakin an kuma gano bama-bamai guda huɗu, bindigar AK-47 guda biyu da kuma batiri mai ƙarfin 75-volt.

More from this stream

Recomended