
Dakarun rundunar sojan Najeriya Operation Whirl Stroke(OPWS) da sauran jami’an tsaro dake aikin samar da tsaro a jihar Benue sun samu nasarar kama wasu mutane biyu dake dauke da bindiga a ranar Laraba lokacin da suke gudanar da aikin sintirin hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta bayyana cewa Felix Agbako wani manomi mai shekaru 42 daga kauyen Abiam a karamar hukumar Gwer East ta jihar da kuma Mr. Tsekaa Kyaan shima mai shekaru 42 wanda direba ne daga kauyen Tse Dam a karamar hukumar Makurdi ta jihar sun shiga hannun dakarun akan wata muhimmiyar hanya ta shiga da fita birnin Makurdi.
A bubuwan da aka samu tare da su sun hada da bindiga kirar AK-47 da kuma kwanson gidan harsashi dake makare da harsashi da kuma wata mota kirar Toyota Camry.
Jihar Benue dai na daga cikin jihohin dake fuskantar hare-hare daga yan bindiga inda a yan kwanakin da suka wuce shugaban kasa Bola Ahmad ya ziyarci jihar bayan kisan da aka yiwa mutane sama da 100 a kauyen Yelewata dake jihar.