
Jami’an tsaro sun kama wani mutum da ake zargin wakilin wata jam’iyar siyasa ne dauke da zunzurutun kudi da yawansu ya kai miliyan ₦25.9 da ake zargin za ayi amfani da su ne wajen sayen kuri’a a zaben cike gurbi da ake gudanarwa a jihar Kaduna.
Mutumin da ake zargi mai suna Shehu Aliyu Patangi an kama shi ne da misalin karfe 03:30 na daren ranar Juma’a a wani otal dake kan titin Turunku a birnin Kaduna.
Jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ne da hadin gwiwa wasu jami’an tsaro suka samu nasarar kama mutumin.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ya ce jumullar kudi miliyan ₦25,963,000 aka samu a tare da shi da aka yi ittifakin za ayi amfani da su ne wajen sayen kuri’a a zaben cike gurbin dan majalisar wakilai ta tarayya a kananan hukumomin Chikun/Kajuru dake jihar ta Kaduna.