
Dakarun Sojan Najeriya rundunar runduna ta 6 sun samu nasarar kama barayin danyen man fetur su 69 a yankin Neja Delta.
Har ila dakarun sojan sun samu nasarar kwace lita 32,000 na man da aka tace.
Hakan na zuwa ne dai-dai lokacin da rundunar ke cigaba da zafafa yakin da take satar danyen man fetur a yankin na Neja Delta.
Mai rikon muƙamin mataimakin daraktan yada labarai na rundunar sojan shiya ta 6, Jonah Danjuma ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi da daddare a Fatakwal.
Danjuma ya ce an kama mutanen ne a tsakanin ranakun 11 zuwa 24 ga watan Agusta tare da hadin gwiwa sauran jami’an tsaro.