Jami’an tsaro sun kama  ƴan gwan-gwan a Abuja

Tawagar jami’an tsaron haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja sun kai samame kasuwannin Panteka da ake kasuwancin kayan gwangwan a birnin tarayya Abuja.

A yayin samamen jami’an sun samu nasarar kayayyakin gwamnati da aka sace dama na kamfanoni da jama’ar gari da kuɗin su ya haura biliyan 1.

Jami’an tsaron sun kuma samu nasarar kama mutane sama da 31 a yayin samamen.

Birnin tarayya Abuja ya jima yana fuskantar sace-sace musamman na ƙarafen murafun kwatar dake kwashe bahayar gidajen birnin.

Kwamshinan ƴan sandan birnin, Olatunji Disu shi ne ya  bayyana haka a lokacin da yake nunawa ƴan jaridu mutanen da kuma kayan da suka sata.

Disu ya gargadi mutane da su guji sayen kayan  sata daga ƴan yawon bola kana su tabbatar sun san daga ina kaya suka fito kafin su saya.

More from this stream

Recomended