Jami’an tsaron da ke gadin majalisar dokokin jihar Rivers sun hana Gwamna Siminalayi Fubara shiga zauren majalisar bayan sun rufe ƙofofin shiga.
A cikin wani bidiyo da sakataren yaɗa labaran gwamnan ya wallafa a Facebook, an bayyana cewa Fubara ya nufi majalisar ne domin gabatar da kasafin kuɗin jihar na 2025.
Rahotanni daga birnin Fatakwal sun nuna cewa jami’an tsaro da aka jibge a harabar majalisar sun ƙi buɗe ƙofofi lokacin da gwamnan ya isa tare da tawagarsa domin gabatar da kasafin kuɗi.
Bayanai sun ambato jami’an tsaron suna cewa ba su da masaniya kan zuwan gwamnan a hukumance, don haka suka dakatar da shi.
Sai dai Fubara ya ce tun a baya ya aika wa kakakin majalisar, Martins Amaewhule, wasikar sanar da shi zuwansa, kuma ya yi ƙoƙarin kiransa a waya tun ranar Talata.
A baya-bayan nan, Kotun Ƙoli ta hana Babban Bankin Najeriya (CBN) ba da kaso na kuɗaɗen jihar daga asusun tarayya saboda rashin gabatar da kasafin kuɗi ga halastacciyar majalisar dokokin jihar.
Haka kuma, kotun ta yanke hukuncin maido da ƴan majalisar dokokin jihar 27 da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC, tare da soke zaɓen ƙananan hukumomin jihar.
Jami’an Tsaro Sun Hana Gwamnan Rivers Shiga Majalisa
