Jami’an tsaro sun gano makamai masu yawa a Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Idris Ododo ya sanar da gano wasu tarin bindigogi da harsashi daga wasu maboyan batagari dake jihar.

Da yake magana da yan jaridu a gidan gwamnatin jihar dake Lokoja a ranar Talata ya ce an samu wannan  nasara ne sakamakon zafafa sanya idanu cikin sirriĀ  da jami’an tsaro suke yi tare hadin gwiwar gwamnatin jihar.

Gwamnan ya ce an sake mayar da hankali ne kan fatattakar bata gari bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu wanda ya shawarce shi da ya mayar da hankali kan shawo kan matsalar tsaro mai makon neman a samun yabo.

“Da na gana da shugaban kasa na yi tsammanin zan samu yabo amma sai ya ce na koma na sake dagewa kan al’ummata,” ya ce.

Ya ce jami’an tsaro sun tsara kai farmaki maboyan batagarin da daddare inda suka samu nasarar gano tarin makaman.

Ododo ya bayyana cewa duk da nasarar gano makaman da aka samu ba a ci nasarar kama koda mutum guda ba daga cikin bata garin.

Jihar Kogi dai na daga cikin jihohin dake fama da yin garkuwa da mutane fashi da makami da ga wasu batagari.

More from this stream

Recomended