Jami’an tsaro sun cafke wani mai yi wa ƴanbindiga safarar kakin soja

Wani farmaki da ‘yan sanda suka kai a kan babbar hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna, ya kai ga kama wani da ake zargi da kayyakin sojan da ba a dinka ba guda 15, wanda za a kai wa ‘yan fashi.

Mansir Hassan, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Kaduna. 

Wanda ake zargin ya amsa cewa zai kai kayan ne wa wani a kauyen Udawa, sannan zai mika su ga ‘yan fashi a yankin Chukuba da ke karkashin karamar hukumar Shiroro a jihar Neja domin gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “A halin yanzu wanda ake zargin yana ba ‘yan sanda hadin kai domin cafke sauran wadanda ake zargi da aikata laifin.

More from this stream

Recomended