Jami’an tsaro a kasar Russia na cigaba da kama mutanen dake zanga-zangar adawa da yakin da kasar take da Ukraine.
A birane da dama dake kasar mutane sun fito kan titunan domin nuna adawar su da yakin.
Mutane na cewa yan kasar Ukraine yan uwansu ne kuma bai dace ace kasarsu tana yakar su ba.