
Jami’ai uku na hukumar NDLEA dake yaƙi da hana sha da fataucin miyagun kwayoyi aka kwantar asibitin sakamakon raunin harbin bindiga da suka samu lokacin da wasu suka farmasu a yayin wani samame da suka kai yankin Jahi dake birnin tarayya Abuja ranar Alhamis da daddare.
Lamarin ya faru ne lokacin da jami’an na NDLEA bisa dogaro da bayanan sirri suka kai samame wani gida da ba a kammala ba a yankin NNPC dake Jahi inda suka gano kwalaben Kodin 74, giram 48 na ƙwayar Tramadol, lita 10 ruwan maganin tari da kuma nau’in tabar wiwi mai ƙarfi da ake kira da Skunk tare da wayoyi biyar ƙirar android.
A dai-dai lokacin da jami’an na NDLEA suke fita daga ginin ne suka fuskanci ruwan wuta daga wasu ƴan bindiga.
Uku daga cikin jami’an na NDLEA sun samu raunin harbin bindiga ɗaya a kirji sauran biyun kuma a ƙafarsu da kuma hannu.
Shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya yi magana da jami’an ta wayar inda ya yi musu addu’ar samun sauki cikin gaggawa.