Jami’an NCSDC sun kama jabun kudade a Maiduguri

Hukumar tsaro ta Civil Defence a jihar Borno ta ce ta gano kudin jabu da yawansu ya kai dalar Amurika 144,000 a wani gida da ba a kammala ba a rukunin gidaje na Shagari dake Borno.

Kwamandan hukumar, Ibrahim Abdullahi shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da ya yi da kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ranar Juma’a a Maiduguri.

Abdullahi ya ce wani birkila dan shekara 40 mai suna, Bukar Goni shine ya gano kuɗin jabun a gidan da ba a kammala ba dake rukunin gidaje na Shagari ranar 16 ga watan Satumba inda ya kai wa hukumar rahoto.

A cewarsa jami’an hukumar sun bincike ginin inda suka gano kudin na jabu.

“Binciken farko da jami’an hukumar suka gudanar ya nuna cewa kudin na dauke da namba iri daya,”

“Haka kuma wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar canjin kudi sun ce sun gano kudaden suna zagawa a kasuwar canjin kudade watannin baya da suka wuce.”

More from this stream

Recomended