Jami’an Civil Defence sun kama ɓarayi 108 a Kano

Hukumar tsaro ta NSCDC da aka fi sani da Civil Defence shiyar jihar Kano ta ce ɓarayi masu ɓarnata kayan jama’a da na gwamnati su 108 aka kama a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a birnin.

Mohammed Lawal Falala kwamandan hukumar na jihar Kano shi ne ya bayyana haka lokacin da yake baje kolin mutanen da ake zargin a ranar Asabar inda ya ce an kama su ne a wurare daban-daban a jihar.

Lawal Falala ya ce an kama mutanen ne biyo bayan ƙwararan bayanan sirri da rundunar ta samu daga sashen ta dake gudanar da bincike.

Ya ce wasu daga cikin waɗanda aka kama ɗin sun fito ne daga maƙotan jihohi sauran kuma sun fito daga jamhuriyar Nijar.

Kayayyaki da dama aka samu a hannun mutanen ciki har da babban injin wutar lantarki ƙirar Mikano da wasu suka sace a unguwar Ɗorayi.

More from this stream

Recomended