Jama’a su yi koyi da jami’an tsaron Legas – Buhari

[ad_1]

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Hakkin mallakar hoto
Getty Images

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya yaba wa wasu jami’an tsaro biyu na filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas dangane da kawo wata jaka makare da kudade da sauran abubuwa masu muhimmanci da wata fasinja ta manta.

Shugaban ya ce wadannan jami’an tsaro wato Francis Emepueaku da Achi Daniel, sun yi “namijin kokari,” san nan kuma sun nuna halayya ta gari wadda za ta zamo “abin kwatance.”

Gaskiya da amannar da jami’an tsaron suka nuna, ta sanya shugaban fitar da sanarwa inda ya ce sun zamo abin koyi ga dukkan ‘yan Najeriya.

Muhammadu Buhari ya ce “Gaskiya da rikon amana ita ce hanya madaidaiciya ga dukkan ‘yan Najeriya, kuma yana da kyau a duk inda muke ko kuma kowanne irin mukami muke rike da shi mu rinka kwatanta gaskiya.”

Jakar dai ta wani likita ce mazaunin jihar Lagos wato Dokta Banji Oyegbami wanda ya dawo daga Amurka, wadda aka manta a filin jirgin saman, kuma tana dauke da abubuwa da suka kunshi makudan dalolin Amurka da wayar salula da agogon hannu mai tsada da kuma sauransu.

Har ila yau jami’an tsaron dai sun ki karbar kudin tukwicin da aka ba su, inda suka ce “sun yi aikin da ya rataya ne a kansu.”

Yaki da cin hanci da rashawa, na daga cikin manyan manufofin da shugaban ya ce ya fi bai wa fifiko a cikin mulkinsa.

Karanta wasu karin labaran

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...