Jakadan Najeriya a kasar Qatar ya rasu

Abdullahi Wase, jakadan Najeriya a kasar Qatar ya rigamu gidan gaskiya.

Tope Elias-Fatile mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasarnan shine ya bayyana mutuwarsa cikin wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce Wase ya yi rashin lafiya na wani dan lokaci kafin rasuwarsa ranar Juma’a da daddare.

“Za a binne marigayin yau a Doha babban birnin kasar da misalin karfe 7:30 na yamma agogon can,”ya ce.

“Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama ya kadu matuka da samun labarin mutuwarsa inda ya yi addu’ar Allah ya bawa iyalansa da ma kasarnan hakurin jure wannan babban rashin,”

Wase na daya daga cikin jakadun da shugaban kasa Muhammad Buhari ya na da su cikin watan Yulin shekarar 2016, kuma ya fito ne daga jihar Plataeu.

More News

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riƙaƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 ƙirar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...