Isa Dogonyaro wakilin al’ummar ƙananan hukumomin Garki da Baɓura a majalisar wakilai ta tarayya ya rasu.
Ɗaya daga cikin abokan aikin marigayin a majalisar tarayya, Bello El-Rufai ya sanar da mutuwar Isa Dogon Yaro cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar ranar Juma’a.
El-Rufai ya bayyana marigayin a matsayin ɗan majalisar mai hazaƙa kuma mutumin kirki.
Shima fitaccen ɗan jaridar nan mamallakin jaridar Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar ya sanar da rasuwar marigayin a shafinsa na Facebook.
Mataimakin mai magana da yawun majalisar wakilai, Philip Agbese ya tabbatar da mutuwar marigayin inda ya ce ya samu labarin mutuwar marigayin ta social media da kuma group na su na WhatsApp.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga iyalin marigayin dake bayyana dalilin mutuwarsa.