Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta fara ci gaba da yin rajistar masu zaɓe a duk faɗin ƙasa a farkon zangon shekarar 2025.
Hukumar ta ce za a fara gudanar da aikin a matakin kananan hukumomi, sannan daga baya a miƙa shi zuwa wuraren rajista.
A wata takarda mai kwanan watan 20 ga Nuwamba, 2024, Sakataren hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta nemi kwamishinonin zaɓe na jihohi su shirya wasu abubuwa don gudanar da aikin.
Sanarwar ta ce, “A samar da bayanai game da halin da na’urorin rajistar masu zaɓe na INEC (IVED) da kayan haɗinsu suke a jiha.
“Haka kuma, a bayyana halin da manyan firintoci masu launi da waɗanda ba masu launi ba suke ciki, tare da wadatar fom ɗin rajista da sauran kayan aikin CVR.
“Hukumar na tunanin fara aikin a matakin kananan hukumomi kafin daga bisani a kai shi matakin wuraren rajista.”