Majalisar Ƙasa na duba yiyuwar gyaran kundin tsarin mulkin shekarar 1999 domin bawa hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta INEC damar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi mai makon hukumomin zaɓen jihohi.
Wannan yunkurin na zuwa ne biyo bayan hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke da ya bawa ƙananan hukumomi ƴanci cin gashin kansu biyo bayan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar.
Da yake mayar da martani kan batun a wurin wani taron manema labarai, Sunday Karimi sanata mai wakiltar mazaɓar yammacin jihar Kogi ya ce majalisar ƙasa za ta tabbatar da cewa jihohi sun yi amfani da hukuncin kotu ta hanyar yin gyaran tsarin mulki domin gyara wuraren da suke da sarkakiya.
Karimi ya ce wannan ya haɗa da miƙawa hukumar INEC gudanar da zaɓuka daga hannun hukumomin zaɓen jihohi.
Ɗan majalisar ya ce har yanzu tsuguno bata kare ba domin wasu gwamnonin za su yi adawa da yin haka.