INEC ta mika wa sababbin jam’iyyu 23 takardar rijista

[ad_1]

INEC

Hakkin mallakar hoto
Inec

Image caption

Shugaban INEC yana mika takardun shaida ga shugabannin sababbin jam’iyyun.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kanta INEC ta mika wa wasu sababbin jam’iyyu 23 shaidar rijista.

A wannan watan ne hukumar ta zabe ta yi wa jam’iyyun yiwa rijista.

INEC ta wallafa a shafinta cewa ta karbi bukatar kafa sababbin jam’iyyu 144 daga kungiyoyin siyasa da suke so a mayar da su jam’iyyun siyasa.

Sai dai 23 daga cikin kungiyoyin ne kawai suka cika sharudan da dokokin zaben Najeriya suka shimfida, a cewar INEC.

Hukumar ta zabe ta ce daga wadannan jam’iyyun ta rufe sake yi wa wasu jam’iyyun rijista, har sai bayan zabukan 2019.

A yanzu adadin jam’iyyun kasar ya kai 91 ke nan.

To sai dai wasu ‘yan kasar da dama na ganin jam’iyyun sun yi yawa, kuma ‘yan kasar ba sa bukatar jam’iyyu masu yawa haka.

Akwai dai masu ganin jam’iyyun za su rikitar da masu zabe ne kawai yayin kada kuri’a.

Dokokin Najeriya dai ba su iyakance yawan jam’iyyun da za a iya kafawa a kasar ba, kuma sun tanadi cewa duk wanda ya cika sharuda zai iya samun rijista.

Hukumar zaben dai ta ce sababbin jam’iyyun na da ‘yancin shiga dukkanin zabukan da ke tafe, kuma sun zama daidai da kowace jam’iyya.

Daga cikin jam’iyyun dai APC da PDP ne suka fi girma da kuma karfi, kuma su kadai ne suka yi mulkin Najeriya tun bayan komawar kasar tsarin dimokradiyya a 1999.

Sababbin jam’iyyun da INEC ta yi wa rijista

1. Advanced Alliance Party AAP

2. Advanced Nigeria Democratic Party ANDP

3. African Action Congress AAC

4. Alliance for a United Nigeria AUN

5. Alliance of Social Democrats ASD

6. Alliance National Party ANP

7. Allied People’s Movement APM

8. Alternative Party of Nigeria APN

9. Change Nigeria Party CNP

10. Congress Of Patriots COP

11. Liberation Movement LM

12. Movement for Restoration and Defence of Democracy MRDD

13. Nigeria Community Movement Party NCMP

14. Nigeria for Democracy NFD

15. Peoples Coalition Party PCP

16. Reform and Advancement Party RAP

17. Save Nigeria Congress SNC

18. United Patriots UP

19. United Peoples Congress UPC

20. We The People Nigeria WTPN

21. YES Electorates Solidarity YES

22. Youth Party YP

23. Zenith Labour Party

Hakkin mallakar hoto
INEC

Image caption

Shugabannin sababbin jam’iyyun ne suka karbi takardar shaidar rijistar daga shugaban hukumar ta INEC

[ad_2]

More News

Obasanjo ya kai wa Remi Tinubu ziyara

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya kai ziyara ga, Oluremi Tinubu mai ɗakin shugaban ƙasa,Bola Ahmad Tinubu . Obasanjo ya ziyarci matar shugaban ƙasar a...

Shehin Musulunci ya nemi masu kuÉ—i da su raba wa talakawa naman Salla

Mataimakin Babban Limamin Masallacin Yobe da Cibiyar Musulunci, Malam Mohammad Ali Goni Kamsulum, ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika...

Ƴansandan sun yi artabu da ƴanbindiga a Abuja

Jami’an ‘yan sanda daga babban birnin tarayya Abuja sun kashe wani dan bindiga tare da cafke uku a wani samame da suka kai.Ƴan sandan...

An wallafa sunaye da hoton fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Suleja

Hukumar NCoS dake lura da gidajen gyaran hali da tarbiyya ta fitar da sunaye da kuma hotuna na É—aurarrun da suka tsere da gidan...