Wasu Iyalai a Kenya na samun abinci sau daya kawai a rana, a wasu lokutan ma ba sa samu saboda karuwar hauhawar farashin kayan abinci, kamar yadda wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga ta ruwaito daga Nairobi.
Da sanyin safiya, na yi kacibis da Florence Kambua tsugune a wani wuri, tana kallo ta wajen kofar dakinta domin karbar robobi da gilasai da tufafi – tana sayar da su a Nairobi, babban birnin Kenya.
Matar, mai shekara 40, tana sanye ne da wata bakar rigar sanyi da manyan takalma na roba.
Aikinta ba na ragaye ba ne. Yana da hadari sosai.
Abincin da ya baci ne ya cika ko ina inda take tattakawa a kauyen Mukuru Kwa Njenga.
‘Wani lokaci za ka kamu da cutar gudawa, wasu lokutan kuma ka kamu da ciwon kirji. Na jajirce sosai saboda ba ni da zabi,’ in ji Ms Kambula.
Matar, mai ‘ya’ya shida, ta sha fama da wahalhalu da dama na rayuwa.
Ta je Nairobi, babban birnin kasar Kenya, shekara19 da suka wuce da fatan samun rayuwa mai inganci
A wancan lokaci, ta rasa aikinta, mijinta ya gudu ya bar ta ba tare da komai ba.
Abin da take yi a yanzu shi ne zabi kadai da zai samar mata da dorewar rayuwa.
Tana samun shilling 100 na kudin Kenya a kowace rana.
Duk da wannan kudi da take samu, Ms Kambua ta ce tana iya bakin kokarinta wajen ganin ta ciyar da iyalanta sau biyu a rana kafin farashin kayan abinci ya tashi.
“Yara na son shinkafa, nakan tafi sayayya da shilling 50 zuwa kasuwa domin sayen rabin kilo na shinkafa sannan na dafa musu.
A yanzu, ba ka isa ka samu shinkafa a farashin ba”.
Garin masara
Yanzu, Ms Kambua ta koma dafa wani sanannen garin masara, wanda ake dafa shi sosai da ake kira Ugali da mutum yakan ci ya koshi, sai dai shi ma a yanzu farashinsa ya tashi sama.
Saboda haka, yanzu tana ciyar da iyalanta sau daya a rana, wani lokacin ma ba sa samun na kai wa bakin salati.
“Ina sayen gari mafi arha a kan shilling 85. Yanzu kuma, garin ya kai shilling 150. A lokacin da ba na samun kudi, muna kwana da yunwa.
Wasu makonni bayan haduwarmu, Ms Kambua ta ci gaba da shiga cikin wahala, inda farashin kilo biyu na garin masara a yanzu ya zarce shilling 200, inda ya karu da kashi 25.
Sabbin alkaluma daga hukumar kididdiga ta kasar Kenya sun nuna karuwar farashin.
Farashin kayan abinci ya ninka sau biyu, inda farashin ya yi sama da kashi 12.4 a watan Mayun 2022 kan yadda suke a watan Mayun 2021.
Magidanta a Kenya da dama na cin masara da ake nomawa a kasar da kuma wadda kuma ake shigo da ita daga makwabtan kasashe.
Wasu lokutan zabin mai sauki ne, sai dai Kennedy Nyagah, shugaban kungiyar masu sarrafa kayan hatsi, ya ce a yanzu ana samun gibi.
“Zan ta’allaka gibin da ake samu da rashin samun wadataccen ruwan sama da kuma tashin farashin kayan gona kamar taki,” a cewarsa.
Kasuwa ta yi kasa
A kasuwar da Ms Kambua take zuwa, harkokin kasuwanci sun yi kasa.
A ziyarar da na kai kasuwar sau biyu, kwastomomi na sayen albasa da tumatiri guda daya-daya saboda sun yi tsada.
“A baya, tumatiri da muke sayarwa a kan shilling 10, muna sayar da shi ne kan shilling 5, ” kamar yadda wani dan kasuwa, Elijah Machuki Nyabutohe ya shaida min, inda yake nuna wani bokiti.
Ya ce: “Shi ya sa yanzu babu masu saye. Suna fargabar cewa idan suka sayi tumatiri da yawa, ba za su samu kudin sayen garin masara ba wanda hakan kan sa su kwana da yunwa.”
Duk da cewa yana da nisa da Ukraine, yana sane da tasirin da yakin da ake gwabzawa a kasar ya yi da kuma yadda ya sanya tashin kudin man fetur da taki.
“Manoma na kashe makudan kudade wajen sayan taki da za su zuba wa tumatirinsu.
“Mutane da yawa kan daina noman tumatiri, saboda sadar taki da kuma irin tumatirin, ” Mr Nyabutohe ya fada min.
‘Yan mitoci kadan daga wajen kasuwar, akwai wata mata, Catherine Kanini – ba ta da aikin yi bayan rushe gidan sayar da barasa da take yi wa aiki domin fadada wata hanya.
Rashin karfi
Matar, mai shekara 30, ba ta da karfin kama hayar gida don haka ta gina wa kanta wani dan karamin matsuguni da ta hada da gidajen sauro da fallen robobi da kuma dirka.
Ta fito ne daga yankin Kitui da ke gabashin Kenya, kamar sauran mutane da ke rayuwa a birane da kudade kadan da ke shigo musu, ita ma Catherine ta dogara ne da taimakon ‘yan uwanta daga gida a lokacin da farashin kayan abinci ke hauhawa.
Mahaifiyarta na aiko mata da abinci daga kauye. Sai dai fari da aka dade ana fama da shi, na nufin cewa da wuya a yanzu ta sami kayan abinci.
“A yanzu, ko ina a bushe a kauyenmu. Babu ruwan sama. Sai an samu ruwan sama sannan mahaifiyata ke samun damar aiko min da abinci,” Ms Kanini ta fada.
“Yanzu, tana sa ran mu aika mata wani abu. Tana dogaro ne da mu, duk da cewa mu din ma muna da matsaloli a nan.”
Tsadar rayuwa da ake fuskanta na zuwa ne a daidai lokacin da Kenya ke shirin gudanar da babban zabe ran 9 ga watan Augusta.
Lamarin na kan gaba a yakin neman zaben manyan ‘yan takara biyu da ke gaba-gaba domin gadar shugaba Uhuru Kenyatta.
Mataimakin shugaban kasa, William Ruto, ya ce lokaci ya yi da za a farfado da tattalin arzikin kasar, yayin da jagoran bangaren adawa Raila Odinga ya yi alkawarin tallafin kudade zuwa ga magidanta da ke fama da talauci a kasar.
Shawara ga iyalai
A shawar da Ms Kanini ta bai wa ‘yan siyasar kasar ta ce “Zan ba da shawarar cewa su bude kamfanoni tare da ba mu aiki. Su kuma rage kudaden kayan masarufi da suka kara. Saboda idan ka samu ‘yan kudade, za ka iya fita domin samo abinci.”
Wani mai sharhi na kungiyar International Crisis Group, Meron Elias, ya yi gargadin cewa yanayin sadar rayuwa zai haifar da rashin tabbas, musamman ma a fafatawar da za a yi a zabukan kasar.
“Duk da cewa ba a san yadda za ta kasance a zabukan kasar ba – a dimokuradiyyar kasar Kenya – muna fargabar cewa matsalar hauhawar farashin kayan abinci da sadar rayuwa a kasar, zai sanya ‘yan siyasa su tara dimbin jama’a kan tituna.
Akwai kuma barazanar cewa za a yi amfani da matasa marasa aikin yi domin bangar siyasa wajen tayar da hargitsi lokacin gudanar da zabe.”