Ina sassarfa fiye da mil guda a rana amma bazan nemi yan Najeriya su zaɓe ni saboda haka ba -Atiku

[ad_1]








Toshon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya takali shugaban kasa, Muhammad Buhari kan maganar dake cewa shugaban kasar yana da lafiyar sake tsayawa takara a karo na biyu saboda ya yi tafiyar mita 800 ranar Sallah a Daura.

Batun lafiyar Buhari ya jawo ce-ce kuce da dama inda wasu dake adawa dashi su ke neman shugaban da kada ya yi takara a karo na biyu saboda rashin koshin lafiya.

A shekarar da ta gabata shugaban kasar ya shafe kusan kwanaki 150 a birnin London yana jiyar wata cuta da ba a bayyana ba.

Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasar ya nemi wadanda suke adawa da takarar Buhari a karo na biyu kan batun koshin lafiya da su nemi wani batun na daban domin tafiyar da yayi mai tsayi haka ya tabbatar da cewa batun lafiyarsa ba matsala bace.

Amma, Atiku Abubakar ya saka wani hoto a shafinsa na Twitter yana motsa jiki inda ya rubuta “Ina sassarfa fiye da mil daya tare da motsa jiki amma zai zamo mini banbarakwai idan nace yan Najeriya su zaɓe ni saboda haka.”




[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waɗanda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...