Ina rayuwa ne da kuɗin hayar gidana dake Kaduna – Buhari

Tsohon shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya ce yanzu yana rayuwa ne da kuɗin hayar ɗaya daga cikin gidajensa dake Kaduna.

Buhari ya fadi haka ne a ranar Asabar a wurin taron masu ruwa da tsaki na jam’iyar APC a Katsina da aka gudanar gabanin zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar.

Za a gudanar da zaben ne ranar 1 ga watan Fabrairu.

Tsohon shugaban ƙasar ya ce yanzu yafi kwari da lafiya fiye da lokacin da yake kan mulki.

Buhari wanda ya mulki Najeriya daga shekarar 2015-2023 ya ce bai azirta kansa ba lokacin da yake kan mulki inda ya ce yana da gidaje uku ke kadai ɗaya a Daura sai kuma biyu a Kaduna.

Ya ce da yawa daga cikin ƴan Najeriya basu da masaniyar kalubalen dake tattare da mulki  suna ɗora laifi kan shugabanin ba tare da sun fahimci cewa Najeriya tana da sarkakiyar mulki.

“Najeriya ƙasa ce da take da wuyar mulka amma yawancin ƴan Najeriya basu san haka ba,” a cewar tsohon shugaban.

More from this stream

Recomended