Ina jin ƙwarin gwiwar cin zaɓe a 2027—Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) na kasa, Rabi’u Kwankwaso, ya bayyana fatansa game da makomar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2027 mai zuwa. 

A cewar wani labari da kamfanin dillancin labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito, tsohon gwamnan na jihar Kano ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP ta shirya tsaf don karbar ragamar shugabancin kasa, da gwamnatocin jihohi da sauran manyan mukamai a fadin kasar nan a 2027.

Sanarwar ta Kwankwaso ta kara jaddada aniyar jam’iyyar NNPP na samun nasara a zabe mai zuwa.

Kwankwaso dai ya je Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya ga iyalan ‘Yar’Adua bisa rasuwar mahaifiyarsu Hajiya Dada.

Ya ce, “Ina so in tunatar da ku cewa jam’iyyar PDP ta riga ta mutu, saboda muna cikin jam’iyyar, tunda sun fita daga kan layi, mun yanke shawarar fita.

 
Ya yi kira ga ’yan Najeriya musamman mata da matasa da kada su bari a yaudare su da “taliya ko kudi a lokacin zabe mai zuwa’’.

 

More from this stream

Recomended