Sanata Suleiman Hunkuyi, dake wakiltar mazabar arewacin Kaduna a majalisar dattawa ya lashe zaben fidda gwanin tikitin takarar sanata a jam’iyar PDP da aka yi.
A makon da ya gabata ne sanatan ya yi rashin nasara a zaben fidda gwani na yan takarar gwamnan jihar Kaduna inda, Isa Ashiru Kudan ya kayar da shi.
Jam’iyar ta bashi dama yin takarar sanata a matsayinsa na daya daga cikin sanatocin da suka sauya sheka daga jam’iyar APC mai mulki.
Hunkuyi ya shiga takarar ne da sauran yan takara biyu da suka hada da Jafar Muhammad da kuma Bilkisu Soba.
Tsohon dantakarar gwamnan ya lashe zaben da ƙuri’u 158 zaben ya gudana a ofishin jam’iyar PDP yankin Zariya.