Hukumar Zaben Nigeria Ta Kara Wa’adin Yin Rajista Zuwa Karshen Wata

[ad_1]

Hukumar zaben Nigeria INEC ta kara wa’adin lokacin rajistar zabe daga ranar 17 ga watan nan zuwa 31 ga wata.

Hukumar ta dau wannan mataki don lura da yadda mutane ke fitowa don neman rajistar, yayin da wa’adin ya kusa karewa.

Ana wannan aikin na rijistar a kananan hukumomin kasar 774 da karin cibiyoyi 672.

Sanarwa daga kwamishinan wayar da kan masu kada kuri’a Muhammed Haruna, ta ce za a ci gaba da yin rajistar in ban da ranakun hutu kamar lokacin murnar babbar sallah.

Zuwa yanzu hukumar ta yiwa mutane miliyan 12,139,061, tun fara shirin a bara.

Mutane da dama da su ka fita domin samun rajistar sun bukaci karin wa’adin don hakan ya ba su damar samun katin saboda su zabi wanda su ke so a 2019.

Kazalika, hukumar zaben ta amince da yi wa karin jam’iyyun siyasa 23 rajista cikin adadin kungiyoyi masu neman rajistar 144.

Da wannan karin dai yanzu adadin jam’iyyun siyasa a Nigeria sun kai 91.

Daga wadannan jam’iyyu da za a dora kan takardar dangwala kuri’a, ba za a sake yi wa wata jam’iya rijista ba sai bayan zaben 2019.

A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...