Hukumar Kwastam Ta Kama  Harsashi Na Miliyan ₦500 Da Aka Ɓoye A Buhunan Garin Kwaki

Hukumar Kwastam ta Najeriya shiya ta ɗaya dake jihar Ogun  ta ce ta kama harsashi 940 da darajarsa ta kai miliyan ₦557,120,828.

Hukumar ta Kwastam ta ce an ɓoye harshin ne a cikin buhunan garin kwaki inda aka yi kokarin shigo da su Najeriya ta kan iyakar Idi Iroko.

Da yake magana da ƴan jaridu a ranar Juma’a, kwantirolsn shiya na rundunar,Ahmadu Shuaibu ya ce an kama kayan ne a ranar 14 ga watan Maris lokacin da jami’an hukumar suke gudanar da sinitirin yaƙi da fasa ƙwauri akan iyaka.

Ya ce hukumar ta kwashe sama da makonni biyu tana bibiyar gungun masu fasa ƙaurin daga jamhuriyar Benin.

Shu’aibu ya ce a lokacin da suke bibiyar gungun masu fasa ƙwaurin ne bayanan sirri sun nuna yadda suke ƙoƙarin boyewa kayan domin gudun kada a kama su.

More from this stream

Recomended