Hukumar Kiyaye Hatsari ta Najeriya ta Tura Jami’ai 35,000 Don sa Ido Akan Tituna

[ad_1]

Jami’an, da su ka hada da cikakkun ma’aikata da na sa kai tuni suka fara aiki ta hanyar duba lasisin tuki, lafiyar tayu, da hana gudun tsiya, da sauran su.

Hukumar ta ce ta tura jami’an don sa ido a wurare masu cike da hadari 45 a kan hanyoyin kamar hanyar Akwanga-Lafiya-Makurdi, Jos-Bauchi-Gombe, Sokoto-Tambuwal-Jega-Birnin Kebbi, Katsina-Kano-Wudil-Dutse-Azare-Potiskum, Kaduna-Saminaka-Jos, Abuja-Kaduna-Kano, Okene-Ogori-Isua-Owo corridor, Makurdi-Otukpo-Obollo Afor-9th Mile, Asaba-Abraka-Ughelli-Warri , Ibadan-Ogere-Sagamu , Sagamu-Mowe-Lago da sauran manyan hanyoyi.

Shugaban hukumar kiyaye hatsurran Bobboyi Oyeyemi na nuna damuwa akan yadda manyan motoci kan janyo munanan hatsari.

“Fiye da kashi 90% na manyan motocin dake kan tituna a Najeriya sun fi shekaru 20 da kerawa don haka su kan haddasa hatsari,” a cewar Oyeyemi.

Sulaiman Danzaki jami’in kungiyar direbobin manyan mota ne, ya yi fashin baki akan yadda motocin ke aiki da kuma yadda ya kamata direbbobi su yi tuki.

Ganganci na daya daga manyan dalilan da kan haddasa hatsari a titunan Najeriya da kuma sanya shingayen ‘yan sanda a wuraren ba a tsammanin samun su.

Saurari cikakken tahoton Nasiru Adamu Elhikaya

[ad_2]

More News

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...

Mutane 18 sun ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota

Aƙalla fasinjoji 18 ne suka ƙone ƙurmus a wani hatsarin mota da ya faru akan babbar hanyar Ojebu-Ode zuwa Ore a yankin Ogbere dake...