Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wasu mutane 643 da aka samu da yin barace-barace a wasu tituna na birnin jihar.
Ana zargin su ne da karya dokar jihar da aka kafa a watan Fabrairu da ta hana yin bara a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar,Lawan Ibrahim ya ce an kama mutanen ne a yankin Bata,titin Murtala Muhammad, Asibitin Nasarawa, Tashar jirgin kasa da kuma gaban Yahuza suya.
Yace wadanda aka kama sun haɗa da mata 416 da kuma maza 232.
Ibrahim ya ce hukumar zata cigaba da kama marabata da suke cigaba da karya dokar.