Hukumar Daukar Ma’aikatan ‘Yan Sanda ta Najeriya (PSC) ta bayyana cewa har yanzu ba ta fara aikin daukar sabbin jami’an ‘yan sanda na shekarar 2025 ba.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar, Ikechukwu Ani, ya fitar da sanarwa a ranar Asabar inda ya nesanta hukumar daga wani tallan bogi da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda ke ikirarin an fara aikin daukar ma’aikata.
Ani ya ce: “Wannan tallan da ke yawo a yanar gizo ba daga hukumar ya fito ba, kuma ba ya wakiltar tsarin ko manufar sanarwar hukumar idan za ta kaddamar da irin wannan shirin.”
Ya yi kira ga wadanda ke sha’awar shiga aikin ‘yan sanda da su yi hakuri, domin a cewarsa, dole a bi dukkan ka’idojin da doka ta tanada kafin a fara aikin daukar sabbin jami’ai.
Hukumar ta nanata kudirinta na gudanar da wani shiri na daukar ma’aikata wanda zai kasance nagari, gaskiya, kuma adalci zai yi masa jagora.
Hukumar Daukar Ma’aikatan ‘Yan Sanda Ta Gargadi Jama’a Kan Ƴan Damfara
