Hukumar D.S.S Ta Bayyana Yadda Mal Lawal Daura Ya keta Ka’idojin Gwamnati

[ad_1]

Bayan da mukkadashin shugaban Najeriya farfesa Yemi Osinbanjo ya kori mal Lawal Daura a matsayin sa na shugaban hukumar leken asiri ta kasa wato DSS. aka kuma nada Mr Mathew Seyeifa domin ya maye gurbin sa, sabon direkta general din ya gana da manema labaru a Najeriya in da ya tabbatar wa ‘yan kasa zai bi ka’idoji na doka wurin kudanar da aikin sa.

Sabon darektan ya kuma ce za a tabbtarar duk wadanda ke tsare a hannun hukumar an bi doka wurin yi masu shari’a ko a sake su idan hukumar ta tarar basu da laifi.

Wannan jawabi dai yana zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan Najeriya ke cigaba da tsokacin akan ‘yan’uwan su ko abokai da aka kama aka tsare ba tare da bin ka’idoji na doka ba duk da yake a wadansu lokuta kotu tana bada umarnin sakinsu.

Ana dai zargi Mal Lawal Daura da cigaba da rike mutanen da kotu ta bada umarnin sakinsu ba tare da bin kai’da ko hukunce hukunce na kotu ba.

A cikin hirarsu da Sashen hausa, wani lauya mai fafutukar kare hakin bil adama kuma daya daga cikin lawyoyin da suke da irin wannan koken akan Mal Lawal Daura wato Bar. Abdulhamid Muhammed, yayi karin haske dangane da muhimmanci sanarwa da Mr mathew Seyeifa Sabon mukadashin shugaban hukumar leken Asiri ta kasa wato DSS yayi.

Saurari cikakken rahoton Umar Faruk Musa

[ad_2]

More News

Ƴansanda sun kama muggan ƴan fashi da makami

Jami’an hukumar ‘yan sanda reshen Elemoro reshen jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a fashi da makami a...

An kama wasu mutane biyu da hodar ibilis a Lagos

Rundunar ƴan sandan jihar Lagos ta sanar da kama wasu mutane biyu da aka samu ɗauke da ƙunshin hodar ibilis mai yawan gaske. Mai magana...

Ƴan sanda sun kama wani mutum ɗauke da bindigogi 20 a Kaduna

Rundunar Æ´an sandan jihar Kaduna ta ce jami'anta sun kama wani  riÆ™aƙƙen mai safarar bindiga inda aka same shi da bindigogin AK-47 Æ™irar gida...

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...