Hukumar birnin Abuja ta rufe ginin ofishin jam’iyar PDP

Hukumar Birnin Tarayya Abuja FCTA  ta rufe ginin  sakatariyar jam’iyar PDP dake Abuja kan zargin da ake yiwa jam’iyar na gaza biyan harajin kudin kasa.

Ginin dake unguwar Wuse Zone 5 an rufe shi da tsakar ranar Litinin gabanin taron shugabannin jam’iyar da aka shirya gudanarwa a ranar Talata.

Taron na majalisar shugabannin jam’iyar ya hada da gwamnoni masu ci da tsofaffi, tsofaffin shugaban kasa da mataimakinsu, shugaba da kuma sakataren kwamitin amintattun jam’iyar, shugabannin jam’iyar a majalisar kasa.

Har ila yau majalisar ta kunshi shugabannin jam’iyar na jihohi 36 da kuma shugabannin jam’iyar na kasa da kuma wadanda aka kafa jam’iyar da su.

Ana sa ran taron na ranar Talata zai mayar da hankali kan batutuwa da dama ciki har da rikicin cikin gida da yaki ci yaki cinyewa tsawon watanni.

A yayin da sakatariyar jam’iyar ke can a garkame kawo yanzu babu wata sanarwa dake nuna canza wurin da za a gudanar da taron.

More from this stream

Recomended