Wata kungiya mai suna Team New Nigeria ta liƙa fastocin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan abin da ya jawo wasu ke raɗe-raɗin hasashen zai tsaya takara a zaɓen 2027.
Fastocin dake dauke da hoton Jonathan na ɗauke da saƙon “Team New Nigeria 2027:The Goodluck Nigeria Needs – Dr Goodluck Jonathan,” an liƙa su ne a fitattun wuraren da mutane za su gani akan titunan Gyadi-Gyadi, Zoo Road, State Road da sauransu.
Moddibo Nuhu Farakwai shi ne wanda ya jagoranci kaddamar da kwamitin da zai dunƙule bukatun kungiyar wuri guda domin gabatar da manufarsu.
Kawo yanzu dai babu wani bayani dake nuna cewa tsohon shugaban ƙasar ya amince da ayyukan kungiyar.
Ƙoƙarin da jaridar Daily Trust ta yi najin ta bakin, Okechukwu Eze mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasar ya ci tura.