Hisbah ta kama mata masu zaman kansu a Kano kafin Ramadan

Hukumar Hisbah ta Kano

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mata da dama masu zaman kansu a wani mataki na tsabtace jihar kafin Azumin Ramadan.

Hukumar ta kai samame ne a gidajen da ake tara mata masu zaman kansu a birnin Kano da wasu kananan hukumomi.

Babban daraktan a hukumar ta Hisba a Kano Mallam Abba Sufi, ya shaida wa BBC cewa sun kama Mata masu zaman kansu guda 26 a garin Kano kawai kuma har an gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu.

“Kotu ta yanke wa wasu hukuncin daurin shekara daya karkashin dokar hana karuwanci,” in ji shi.

Ya kuma ce sun sun kai samamen a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Tambarawa da suka yi suna wajen tara mata masu zaman kansu.

A Dawakin Dudu hukumar ta ce ta kama mata da dama amma ta yi yarjejeniya da su, inda suka amince su fice daga jihar da ke aiwatar da shari’ar musulunci.

Hisbah a Kano ta kai samamen ne yayin da ya rage ‘yan kwanaki a fara gudanar da azumin watan Ramadana.

Malam Sufi ya ce Kano jiha ce ta addinin musulunci wacce take shari’ar musulunci, kan haka ne kuma hukumar Hisbah ta kaddamar da samamn a wuraren da ake zargi na mata masu zaman kansu ne da wuraren da ake zargi ana ayyukan masha’a.

Ya ce hukumarsu za ta ci gaba da samame a gidajen mata masu zaman kansu domin tsabtace jihar a lokacin watan Ramadan inda ya yi kira ga jama’a su sanar da hukumar gidajen da suka san ana aikata ayyukan masha’a.

More from this stream

Recomended