
Wani mummunan hatsarin mota da ya faru da safiyar ranar Juma’a ya lakume rayukan mutane 12 a kauyen Samawa dake karamar hukumar Garun Mallam ta jihar Kano.
Hatsarin dai ya rutsa ne da wata motar tirela mai namba KMC 931 ZE kirar DAF ita kadai akan titin Kano zuwa Zaria tana kuma dauke ne da mutane da kayayyaki.
A cewar hukumar FRSC dake kiyaye afkuwar hadura a titunan Najeriya ta bakin kwamandan shiyar Kano na rundunar ya ce binciken farko da suka gudanar ya nuna cewa wata matsalar inji motar ta samu har ta kai ga hatsari.
Mutane 19 hatsarin ya rutsa da su inda 12 suka mutu nan take, 5 suka samu raunuka a yayin da mutane biyu suka tsira ba tare da sun ji ciwo ba.
Kwamandan ya ce an garzaya da wadanda suka jikkata asibtin garin Kura a yayin da gawarwakin aka ajiye su asibitin Nasarawa dake kwaryar birnin Kano.
A ziyarar da ya kai wurin da hatsarin ya faru, M.B Bature kwamandan shiyar ya koka kan asarar rayukan da aka yi ina ya ce abu ne da za a iya kaucewa faruwarsa.
Ya alakanta da hatsarin da rashin bin kaidojin tuki da kuma daukar mutane fiye da ka’ida.