Akalla ’yan jarida bakwai ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu hudu suka jikkata sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da motar Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) a Jihar Gombe.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yammacin ranar Litinin yayin da ’yan jaridan ke dawowa daga wani biki a yankin Gombe ta Kudu. Sun kasance cikin tawagar da ta je taya wani abokin aikinsu, ma’aikacin Gidan Talabijin na Kasa (NTA), murnar aure.
Shugaban Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) a Jihar Gombe, Samson Kaura, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutum 11 ne ke cikin motar. “Bakwai sun mutu a wurin, yayin da hudu suka samu raunuka daban-daban,” in ji shi.
Ya kara da cewa binciken farko ya nuna hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar taya, kuma motar ba ta yi karo da wata mota ba.
Hatsarin Mota Ya Hallaka ’Yan Jarida 7 A Gombe

