Harin Boko Haram ya hallaka sojojin Najeriya 30 a Borno

[ad_1]

Sojan Najeriya

Hakkin mallakar hoto
AFP

Rahotanni daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa mayakan Boko Haram sun kai wani hari da yayi sanadiyyar mutuwar sojojin Najeriya akalla 30.

Da alama mayaka masu yawa ne suka kai harin bazata a kan wani sansani sojoji.

Rahotannin sun bayyana cewa akalla sojoji 30 sun rasa rayukansu a lokacin wannan harin bazata da kungiyar BH ta kai kan sanasaninsu.

Da alama gomman mayakan kungiyar ta BH sun isa sansanin sojojin Najeriya ne a cikin manyan motoci dauke da muggan makamai.

Kuma an yi ta nusayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da mayakan kungiyar ta BH na kimanin sa’a guda, kuma wani babban jami’in soji ya bayyana cewa sojoji 30 ne suka mutu.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa mayakan BH sun mamaye sansanin har ma sun tafi da makamai da wasu kayan yaki kafin aka fatattake su da jirgin yaki.

Wani mai magana da yawun sojojin Najeriya ya ce an kashe mayakan BH masu yawa bayan da jirgin yakin ya isa fagen dagar, inda ya rika yi musu luguden wuta.

A watan jiya ma mayakan BH sun kashe kimanin sojojin Najeriay 63 a wani hari da suka kai a yankin na arewa maso gabashin Najeriya.

[ad_2]

More News

Kwankwaso ya bada tallafin miliyan ₦50 ga mutanen da ambaliyar Borno ta shafa

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma jagoran jam'iyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya bada tallafin naira miliyan 50 ga mutanen da ambaliyar ruwa a...

Sakamakon NECOn 2024 ya fito

Hukumar shirya jarabawar ta kasa ta fitar da sakamakon jarabawar kammala sakandare ta watan Yuni/Yuli 2024, inda kashi 60.55 cikin 100 na waÉ—anda suka...

Ƴan Najeriya na shan baƙar wahala—Janar Abdulsalami

Tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalami Abubakar, ya ce wahalhalun da ake fama da su a Najeriya na kara tabarbarewa, kuma rabon kayan agajin ba...

EFCC ta musalta cewa Yahaya Bello na tsare a ofishin hukumar

Hukumar EFCC dake yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa ta'annati ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello baya ya tsare a hannunta. A...