Har yanzu ba a fara ɗebe ƴan Najeriya da ke Sudan ba

Rahotannin da muke samu sun nuna cewa har yanzu ba a fara ɗebe ƴan Najeriya da ke Sudan ba duk da alkawarin da gwamnati ta yi.

In ba a manta ba ana cikin mawuyacin hali a kasar ta Sudan saboda yakin da ake fama da shi wanda ya dauki tsawon makonni.

Jaridar Daily Trust ta ambato shugaban ɗaliban Najeriya da ke Sudan yana cewa har zuwa daren jiya gwamnatin ba ta fara shirye-shiryen ɗebe daliban ba.

Zuwa yanzu dai an hallaka daruruwan mutane a dalilin yaƙin da ya barke tsakanin dakaru masu kare gwamnati da ƴan adawa.

More from this stream

Recomended