Har Yanzu Ana Ci Gaba da Jimamin Mutuwar Ali Kwara

VOA Hausa

Marigayin wanda ya rasu a Abuja, yayin da a ke shirin fita da shi kasar Masar don zuwa wani Asibitin na musamman, an yi jana’izar sa a garin sa Azare da ke jihar Bauchi arewa maso gabashin Najeriya.

Alhaji Ali Kwara kan dade ba a ji duriyar sa ba, amma duk lokacin da ya fito ya kan nuna ‘yan fashi da barayi da ma masu yin sojan gona da sunan sa wanda ya kan kama da damka su hannun ‘yan sanda.

BAUCHI: Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa
BAUCHI: Ali Kwara ya kama barayi masu fashi da makami tare da yin garkuwa da mutane suna karban kudin fansa

A wata zantawa, Ali Kwara ya damke wani mai sojan gona da sunan sa wanda ke cigaba da jagorantar ‘yan banga a yanzu haka. Kwara ya baiyana dabi’un da za a iya tantance shi da ‘yan bogi.

Wasu daga muggan ‘yan fashi da wakilin sashen Hausa ya samu a gidan marigayin mai suna Na- Kutama, ya ce bai san adadin mutanen ya kashe ba.

Acan Azare kuwa, a na ci gaba da zuwa ta’aziyya. Malamin Islamiyya Sabbar Aminu makwabtan gidan Ali Kwara ne da a ka yi jana’izar da shi. Ya ce marigayin ya bar wasiya kafin mutuwarsa.

Shi ma mai sharhi a gidajen rediyo a Bauchi Almustapha Haji Sufi ya ce an yi babban rashin mutum mai gaskiya da amana.

Shin kowaye zai cike gurbin Ali Kwara, a daidai lokacin da lamuran rashin tsaro ke kwan gaba kwan baya?.

More from this stream

Recomended