
Asalin hoton, Aishabuhari
Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari ta wallafa hotunan auren ɗiyarta Hanan, da angonta Mohammed Turad, a shafinta na Instagram.
Ta wallafa hotunan tare da rubuta “#HamadForever Alhamdullilah”
Tun a watan Agustan da ya gabata ne rahotanni suka karaɗe shafukan sada zumuntar ƙasar cewa ƴar Shugaba Muhammadu Buhari, Hanan, za ta auri ɗan fitaccen ɗan siyasar nan a Kaduna Sani Sha’aban wato Mohammed Turad.
An ɗaura auren ne a ranar Juma’a, 4 ga watan Satumba a Fadar Aso rock.
Asalin hoton, Aishabuhari
Asalin hoton, Aisha Buhari IG
Abin da muka sani kan Ango Muhammed Turad
Muhammad Turad Sha’aban, ɗan tsohon ɗan majalisar da ya wakilci yankin Sabon Gari ta Zariya ne a majalisar dokoki ta biyar ta Najeriya, kuma ya yi takarar gwamna a zaɓukan 2007 da 2011.
Alhaji Sani Sha’aban, shi ne yake riƙe da sarautar Ɗamburam a Masarautar Zazzau.
Rahotanni sun ce shi Turad ƙwararre ne a harkokin kuɗi.