Mai taimaka wa Shugaban jam’iyyar PDP na Jihar Zamfara ta fannin yada labarai, Muhammad Isah, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Isah, wanda ya yi aiki karkashin Shugaban PDP na jihar, Hon. Jamil Jibo Magayaki, ya bayyana sauya shekar tasa ne a ranar Litinin, inda ya ce abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar PDP a yanzu ne suka sa ya dauki wannan mataki.
Wani rahoto ya nuna cewa wannan matakin ya zo ne bayan dan takarar PDP a zaben cike gurbi na mazabar Kaura Namoda ta Kudu, Hon. Muhammad Lawal Kurya, ya koma APC makonni kadan da suka gabata, bayan shan kaye a zaben da aka gudanar ranar 21 ga watan Agusta, 2025.
Sauya shekar Isah na kara jaddada karuwar yawan mambobin PDP da ke barin jam’iyyar zuwa APC a Jihar Zamfara, lamarin da ake ganin yana nuna raguwar kwarin gwiwa ga jam’iyyar adawa a jihar.
Hadimin Shugaban PDP Na Zamfara Ya Sauya Sheka Zuwa APC
