Gwamnoni da aka zaba ƙarƙashin jam’iyar PDP sun tattaru a Asaba babban birnin jihar Delta domin su tattauna batutuwan dake damun jam’iyar.
Gwamnonin da suka yi shigar gargajiya irin ta mutanen yankin kudu maso kudu sun gudanar da taron a gidan gwamnatin jihar dake Asaba a ranar Juma’a.
Sun samu tarba daga gwamnan jihar, Sheriff Oborevwori.
Taron na gwamnonin na zuwa ne dai-dai lokacin da jam’iyar ta PDP ke tsaka da fama da rikicin shugabanci da yaƙi ci yaƙi cinyewa.